SHARHI

Bayanin Jerin Matasa da suka kashe kansu akan soyayya a arewacin najeriya da baku sani ba.

Faruwar irin wannan al’amari na kisan kai baƙo ne a kasashen Hausa , sai dai masu sharhi kan tarbiyya na alaƙanta hakan da yawan kalle-kallen fina-finan ƙetare da suka jiɓinci soyayya.

 

1= Abdul

17feb2021 Jami’ar Tarayya da ke Dutse FUD, a jihar Jigawa da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar ɗaya daga cikin ɗalibanta da ake zargin ya kashe kansa bayan wata taƙaddama ta shiga tsakaninsa da budurwarsa.

Ana zargin matashin ya kashe kansa ne ta hanyar shan wani abu da ake zaton guba ce bayan budurwarsa ta zarge shi da kula wata daban ba ita ba.

To sai dai jami’ar ta FUD Dutse ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike kan al’amarin.

Daya daga cikin abokan karatun mamacin ya bayyana cewa al’amarin ya faru ne a unguwar Yalwawa inda marigayin da budurwar tasa da sauran ɗalibai ke haya, bayan ya koma gida daga makaranta.

Haka zalika abokin nasa ya ce matashin ya kashe kansa ne bayan da budurwar tasa da ke aji biyu a sashen tattalin arziki wato Economics, ta ce ta daina soyayya da shi a lokacin da suka je wani wurin cin abinci, a ranar masoya ta duniya a Lahadin da ta gabata, sakamakon ganowa da ta yi cewar yana kula wata bayan ita.

“A ranar Valentine Day ne shi saurayin ya ɗauki budurwar tasa suka je kantin Sahad Store a Dutse. Bayan nan ne sai ita budurwa tasa ta ji labarin cewa ya je ya kula wata ba ita, wannan ne ya jawo hargitis da hatsaniya har suka rashin jituwar da ta ce ta haƙura da shi.

“Wannan taƙaicin rabuwa da shi da ta ce ta yi ne ake tunanin shi Abdul ya sa ya sha wani abu da ya kawo ƙarshen rayuwarsa.

“A ranar Litinin ma ya shiga lakca, bayan nan ne kawai sai aka ji an kwantar da shi a Asibitin Koyarwa na Jami’ar, daga nan kuma sai ya rasu,” a cewar abokin mamacin.

Wannan batu dai ya ja hankulan al’umma a ciki da wajen makarantar musamman ma ɗalibai, da kafafen sada zumanta.

 

2= Ashiru Musa

Yuli 25 2020 Matashi mai shekaru 25 dan asalin jihar Kano mai suna Ashiru Musa Danrimi, ya kashe kansa ta hanyar sokawa cikinsa wuka a jihar Kano.

An gano cewa matashin ya aikata hakan ne bayan budurwarsa da suka zuba soyayya za ta auri wani mutum da ba shi ba. Kamar yadda rahoton ya bayyana, mamacin dan asalin gundumar Kadawa ne da ke karamar hukumar Ungogo ta jihar Kano. Hankalinsa ya tashi kuma ya yi matukar harzuka bayan da ya gano cewa budurwasa mai suna Ummi Muhammad ta yanke hukuncin auran wani mutum daban.

Bincike ya nuna cewa, ya mayar da hankali ba kadan ba a kan soyayyarsu saboda ya sadaukar da kudinsa, aljihunsa da lokacinsa. An zargi cewa ya soka wa kansa wuka bayan samun wannan labarin. A yayin tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin rundunar ‘yan sanda jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce ‘yan sanda sun gaggauta mika shi asibitin kwararru na Murtala da ke Kano inda aka tabbatar da mutuwarsa.

Makwabtan mamacin sun bayyana alhininsu da mamaki a kan aukuwar lamarin, domin kuwa sun san irin soyayyar da ke tsakanin masoyan. Basu taba tsammanin za ta kare a hakan ba.

 

3= Aisha Aminu

9sep2019 Wata matsashiya mai suna Aisha Aminu mazauniyar Albarkawa a jihar Zamfara ta kashe kanta ta hanyar cinnawa kanta wuta saboda an hanata auren saurayin da take so.

Aisha ta rasu ne a ranar Laraba bayan fama da jinya ta fiye da wata guda sakamakon raunukan da ta samu bayan cinna wa kanta wuta da tayi.

saurayin marayiyar ya dimauce domin da kyar a ka dora shi a mota domin ya koma gida.”

Kafin rasuwarta, Aisha ta shaida wa BBC cewa ta dauki wannan mataki ne saboda ba za ta iya hakura da shi ba kuma “da ta yi karuwanci gara ta kashe kanta” kawai.

Mahaifin Aisha Aminu Muhammad Albarkarawa ya shaida wa BBC cewa saurayi ne take so tsawon shekara daya amma Allah bai sa yana da abin aurenta ba.

“Saboda haka ne muka dakatar da shi da zuwa wurinta tunda ba shi da abin aurenta har sai Allah ya kawo mata wani.,” in ji Aminu Muhammad.

Ya kara da cewa: “Ashe ita kuma tana sonsa sosai. Shi ne ta dauki wannan mataki ba tare da saninnmu ba, kawai sai ganinta muka yi tana ci da wuta, jama’a suka tay mu kashe kokarin wutar.

“Da aka tambaye ta dalili sai ta ce ita wallahi tana sonsa ne kuma da ta je ta yi iskanci gara ta kashe kanta tun da ba shi da halin da zai iya aurenta.”

Ita ma Aisha ta ce ta dauki wannan mataki ne saboda tana sonsa kuma shi ma yana sonta.

Ta ce: “Na dauki wannan mataki ne saboda ina sonsa kuma tun da muke tare da shi bai taba gaya mani wata magana ba.

“Acaba (okada) yake yi saboda haka sai ya yi zaton cewa ba shi da wani hali. Ni kuma na ce da in je in yi karuwanci gara na kashe kaina na huta kawai. Sai na sa ma kaina fetur kawai, na sa ashana.”

Aisha ta ce ta ji raunuka a hannayenta da bayanta da kuma ciki, sannan kuma ta ce ta yi nadama.

 

4= Aminah isa

14oct2020 Wata budurwa yar asalin jihar Gombe mai suna Amina Isah Kuma mazauniyar unguwar Bamusa takashe kanta saka makon auren dole da iyayenta suka mata. Kamar yadda Wakilin mu ya tattauna da Wata kawarta ta bayyana Cewa , ita Amina tana soyayyane da wani wanda takeso mai Suna Muhammad , daga bisani kuma iyayenta suka tilasta mata auren wani Wadda bata son sa wadda hakan yakai ga iyayenta sun aura mata wanda suke so alhali kuma ita bata son shi .

Kafin dai budurwar tasha madarar fiya – fiya tamutu tayiwa wasu daga cikin kawayenta Text Massage Wadda suka hada da Hassana , Zahra , Da Aisha , akan cewa itafa muddin aka mata auren dole to wlh zata kashe kanta . Haka kuma tasanarda mahaifinta Malam Isa cewa itafa muddin aka aura mata wanda bataso sai ta kashe kanta , budan bakin mahaifin ta sai yace takashe mana idan hauka takeyi , yarinyar dai kafin gari ya waye tasha fiya fiya ta mutu har lahaira . Muna fatan hakan zaizama izina ga sauran iyaye dasu keyiwa wajen yiwa yaran su auren dole .

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!