SHARHI

Anyi zaben wanda yafi iya aktin a shirin LABARINA kalli wanda ya fita na daya da na karshe

Shirin Labarina shiri ne mai dogon zango da miliyoyin mutane ke ƙallan a fadin duniya ta hanyar gidan television na Arewa24 da kuma tashar youtube ta saira movies, Labarina yana daya daga cikin manyan shirye-shirye da aka fi ƙallan su a duniyar Hausa, ganin jaruman cikinta suna taka rawa yadda ya dace, an gudanar da wani zabe da aka tantance gwarzaye a cikin jaruman ta labarina wa’yanda suka fi iya acting kuma yawan masoya ta hanyar shafukan sada zumunta, a wannan bidiyo zaku ga wanda yayi dace ya fito a na daya da kuma wanda ya fito a na biyar.

 

 5. teema general Tukur. UMMI KARAMA

Ummi karama ta bayyana a shirin Labarina a matsayin wacce take yar uwa ga lukman wacce take matukar son shi, kuma Hajiya babba ta shige gaba kan cewa sai anyiwa lukman da ummi hadin gida wato a musu aure. Wannan rawar da take takawa shi yasa tayi nasara ta zamanto a na 5 cikin wa’yanda suka fi iya acting a shirin na labarina.

 

 4. Nafisa Abdullahi / SUMAYYA

Sumayya itace mai jan ragamar shirin tun farkon fara shi, tasha kalubale daban-daban kamun ta samu daukaka, inda ta kasance yar talakawace da bata tare da mahaifinta a farko, tayi masoyi mai suna Mahmud da ya taimaka mata a asibiti daga nan wani mai suna fresdo ya zamo mata karfen kafa a shirin inda ya hanata samun kwanciyar hankali kasancewa shi ɗan masu kudi ne, kuma yana sonta hakan yasa ya sanya mata sharadin kada ta yadda ya ganta da kowa, shi kuwa wannan fresdo din kashe mutane ba komai bane a gunsa, daga karshe dai sumayya tayi arziki ta inda naziru Sarkin waka ya taimaka mata ta zama babbar mawakiya da ta shahara a duniya, nafisa Abdullahi wato sumayya tabbas mutane suna matukar yaba mata bisa irin rawar da take takawa kamar da gaske, hakan yasa ta samu kuri’u masu yawa da yasa ta zamanto a hudu.

 

3. Fresdo / ISAH FEROZKAN

Fresdo ya kasance dan gidan Alhaji dan gaske wanda yana daya daga cikin masu kudin garin, Alhaji dan gaske fresdo shi kadai ne yaron da Allah SWT ya mallaka masa dangaske, hakan yasa baya son ganin bacin ransa ko kadan, shi yasa fresdo yake rashin mutuncin da yaga dama domin yasan mahaifinsa yana da kudi kuma yana da mukami a siyasa, a shirin ansha bada labarin cewa fresdo yasha kashe mutane babu abinda ake masa kuma da bindigarsa yake yawo daga karshe dai an kama shi an kulle shi inda yaci gidan yari na dan wasu lokuta sannan ya fito, kuma hakan baisa ya rage dabanci da yake ba, to shi dai wannan role da fresdo yake takawa na ta’addanci yana matukar burge mutane hakan yasa a zaben da aka yi shi yayi nasara ya zama na 3 cikin wa’yanda suka fi iya acting a shirin na labarina.

 

2. Maryam waziri / LAYLA

Layla ta taka rawar da zamu iya cewa duk mai bibiyar shirin Labarina sai da ta burge shi, domin a shirin ta Labarina ta fito a matsayin yar gidan masu kudi da bata kyamar talakawa ga kuma yawan Alhairi duk kawayen ta talakawa ita take daukar nawin su, tayi soyayya da Mahmud a yayin da take zaton cewa bashi da wata budurwa alhalin yana budurwa sumayya da ya rabu da ita domin ya samu yar gidan masu kudi wato Layla daga karshe Layla ta gano cewa ashe ba don Allah yake sonta ba domin itama zai iya rabuwa da ita idan ya samu wata, kamar yadda yabar sumayya ya so ta, bugu da kari kuma gashi bashi da asali, wannan rawa Maryam waziri ta taka a matsayin Layla mutane sunji dadinsa matuka hakan yasa tayi nasara ta zamanto a na 2.

 

1. Rabi’u rikadawa / BABA DAN AUDU

Baba dan audu Kenan duk mai bibiyar shirin labarina sai da ya bashi dariya, ya kasance miji ne ga mahaifiyar Mahmud da ya taho a kasar Saudiyya, kuma ya kasance mutum ne mai son abin wani, domin a gunsa ba komai bane ya danfareka duk alakar da kake da shi, shi yasa matar shi wato mamar Mahmud bata daga Mishi kafa kamar ba mijinta ba. Tabbas Rabi’u rikadawa wato baba dan audu kowa ya yaba masa, domin idan yana acting kamar da gaske yake ba a Fim ba, duk cikin shirin Labarina babu wanda ya samu kuri’u masu yawa kamar yadda ya samu, shi yasa yayi nasara ya zamanto a na daya cikin jaruma shirin LABARINA da suka iya acting da kuma yawan masoya.

Domin kallo a bidiyo danna nan 👇👇

 

Mun gode daga AREWA WEB

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!