SHARHI

Kalli jerin jaruman kannywood 10 da suka kasance ba Hausawa ba ne, da kuma asalin kabilar su.

Masana’antar finafinai na kannywood masana’anta ce da ake magana da harshe Hausa amma hakan bai hana wayan da suka kasance ba Hausawa ba, shiga masana’antar ba.

1. Mansura isah.

Mansura isa ta kasance tsohuwar matar jarumin kannywood wato sani Danja, Allah ya basu ‘ya’ya biyar a tare, tsohuwar jarumar da ta koma harkar Film bayan mutuwar auren ta kasance ya kabilar yarabawa ce wata bayarabiya.

2. Maryam waziri.

Duk mai kallan shiri mai dogon zango na arewa24 mai suna labarina yasan da zaman Maryam waziri wacce aka fi sani da Layla a shirin, jarumar haifaffiyar jihar Gombe ta kasance batangaliya ce inda ta bayyana hakan a wata tattaunawa da tayi da Aminu Sharif momo a shirinsa na kudin kannywood.

3. Sani danja.

Sani Danja yana daya daga cikin manyan jarumai da suka goya masana’antar kannywood har ta kai ga wannan lokacin da ta shahara a Duniya, ba lallai bane mutum ya fahimci cewa shi ba bahaushe ba ne idan yana maganar Hausa, sani dai ya kasance bayarabe ne.

4. Amina Amal.

Amal Umar ta kasance cikakkiyar bafulatane ce ta kasar Kamaru, domin a lokacin da tazo kasar Nigeriya domin shiga harkar Film ko Hausa bata ji ko kadan sai da ta dauki a ƙalla shekara daya tana koyon harshen Hausa sannan aka fara sanya ta a finafinai.

5. Ainau ade.

Sama da shekaru 15 aina’u ade tana masana’antar kannywood kuma har wa yanzu tana taka rawa a kannywood, anfi sanin jarumar a masifaffiya a finafinai, ita dai ta kasance bayarabiya ce.

6. Halima Atete.

Jarumar kannywood haifaffiyar jihar Borno mai suna halima atete ta kasance babarbariya ce wadda aka fi sani da kanuri, tana daya daga cikin matan kannywood da suka fi kudi.

7. Hassan Giggs.

Darakta Hassan giggs shima dai ya dade yana bada gudummawa a kannywood ta hanyar bada umarnin finafinai, shima dai bayarabe ne.

8. Maryam gidado

Babbar jarumar masana’antar kannywood wato Maryam ta kasance ba fulatana ce inda, ta bayyana hakan a wata tattaunawa da aka yi da ita, jarumar mai ‘ya’ya 2, har yanzu ana damawa da ita a kannywood

9. Rahama Mk sulayman

Duk mai kallan shirin kwana casa’in mai dogon zango da tashar arewa24 ke haskaka, yasan rahama wacce aka fi sani Hajiya rabi bawa mai kada a shirin ta kwana casa’in, ita ma dai ta kasance bayarabiya

10. Ummi zeezee

Ummi zeezee duk da ta kasance tsohuwar jaruma ce a masana’antar kannywood bai kamata a manta da ita ba, jarumar haifaffiyar garin Maiduguri ce ita yar kabilar kanuri ce, mahifiyarta kuma shuwa Arab.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!