SHARHI

Bidiyo | Yadda aka kashe shuwagabannin africa 20 akan karagar mulki, da kuma tarihin su

Jerin shuwagabannin Afrika da aka yi musu kisan gilla akan karagar mulki da kuma bayanin yadda aka kashe suda manufar da yasa yi hakan.

 

1. John Aguiyi Ironsi, an kashe shi a shekarar 1966.

Aguiyi-Ironsi ya mulki kasar nigeria a matsayin shugaban kasa na tsawon watani shida kafin wasu sojojin su yiwa gwamnatinsa juyin mulki.

A lokacin da ya kai ziyarar rangadi yankin Yammacin Najeriya wanda gidan gwamnatinsa ke Ibadan, a daran wannan rana Aguiyi-Ironsi ya ji kishin-kishin cewa sojoji na shirin yi masa juyin mulki, inda da sanyin safiyar 30 ga watan Yuli, sojojin karkashin jagorancin Theophilus Danjuma suka yiwa gidan gwamnatin da ya kwana a ciki kawanya, inda Danjuma ya ma sa tambayoyi game da juyin mulkin da yakai ga kisan Sardaunan Sokoto, Sir Ahmadu Bello.

Daga bisani an tsinci gawar Aguiyi-Ironsi da gwamnan soji a yankin Yammacin Najeriya wato Laftanal Kanal Adekunle Fajuyi a wani daji dake kusa da garin Badin. An kashe su ne a 1966

 

2. Abdirachid-Ali Shermake 1968 Somalia

A 1968, da kyar Sharmarke ya tsere daga yunkurin kashe shi da aka so yi. Inda Wata gurneti ta fashe kusa da motar da ke dawo da shi daga filin jirgin sama, amma a lokacin ya tsira bai mutu ba.

A ranar 15 ga watan Oktoban 1969, yayin da ya kai ziyarar aiki a garin Laascaanood da ke arewacin kasar , daya daga cikin masu gadin nasa ya harbe Sharmarke har lahira. A bakin aiki a wajen masaukin baki inda shugaban yake, jami’in ya bude shugaban wuta, inda nan take ya kashe Sharmarke. Masu lura da al’amura sunce wannan kisan ya samo asali ne daga wani manufa ba dalilin siyasa ba.

Kisan Sharmarke ya biyo bayan juyin mulkin soji a ranar 21 ga Oktoba, 1969, inda Sojojin Somaliya suka kwace mulki ba tare da fuskantar adawa da makamai ba ko zubda jini ba. Manjo Janar Mohamed Siad Barre shi ne yake jagorantar rundunar a wannan lokacin.

 

3. Abeid Amani Karume 1972 zanzibar

Ya hau kan karagar mulkin zanzibar 1964 zuwa 1972. An kashe Karume a watan Afrilun 1972 a Garin Zanzibar. Wasu ‘yan bindiga hudu suka harbe shi har lahira yayin da yake wasan bao a hedikwatar jam’iyyar Afro-Shirazi . An yi ramuwar gayya kan mutanen da ake zargi suna adawa da gwamnatin Karume. Amani Abeid Karume , ɗan Abeid, an zaɓe shi sau biyu a matsayin shugaban Zanzibar, a cikin 2000 da 2005 da gagarumin rinjaye kuma ya mika mulki a ƙarshen 2010 ga magajinsa Ali Mohamed Shein .

 

4. Mista Francois Ngarata Tombalbaye 1975

Ya yi mulkin ƙasar cadi a lokacin da ta sami ‘yancin kai a ranar 11 ga Agustan 1960. Francois Tombalbaye yayi yunkurin juyawa kasar Faransa baya ta hanyoyi daban-daban a mulkinsa, inda yayi sauye sauye da dama a zamaninsa cikin, hakan yasa jama’ar kasar suka kuncin hali, inda aka kara kudin haraji a saniyar wannan jama’ar kasar sun sha yin zanga-zanga kan nuna adawa da gwamnatinsa, a shekarar 1975 ya kama wasu manyan sojojin kasar bisa zargin su da yayi zasu yi mishi juyin mulki, sannan ya karawa wasu jami’an kasar mukami ba a ka’idance ba, nan wasu manyan sojojin ƙasar suka kama Tombalbaye, sannan suka kashe shi suka binne gawarsa a Faya, sannan aka naɗa général felix maloum a matsayin shugaban kasar cadi.

 

5. Marien Ngouabi

Ya hau kan karagar mulkin congo a shekarar 1968, A wata 18 Maris 1977 da misalin karfe 2:30 na rana aka kashe shugaban kasar congo Ngouabi. An gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a kisan kuma an kashe wasu ciki har da Massamba-Débat wanda yake shima babban jami’in gwamnati ne a lokacin

Bayan kisan, an sanya sunan Kwamitin Soja na Jam’iyyar (CMP) don jagorantar gwamnatin rikon kwarya tare da Kanar Joachim Yhombi-Opango mai rikon kwaryar Shugaban kasa.

 

6. Tafari Bante, Ethiopia 

Ƙungiyar EPRP takasance Jam’iyyar Juyin Juya Halin Habasha, suna adawa da tsohon tsarin mulki da kasar habasha ta kafu a kanta wato mulkin gurguzu, sannan suna bada haɗin kai “ga duk sojojin da suka ƙi tsohon tsarin mulkin ƙasar ta Ethiopia), wanda aka gina daga tushe.

Domin tara Tafari da sauran membobin Derg da ake zargi da hada baki da EPRP. Sai aka gayyace su wani taro na yau da kullun a ranar 3 ga Fabrairu 1977, nan Sojoji a ƙarƙashin jagorancin Laftanar Kanal Daniel suka kama Tafari da sauran membobin Derg da ake zargi da hada baki da EPRP. daga nan aka kai su wani daki mai sananin duhu aka kullesu, bayan wasu lokuta sai wasu mutane hudu suka shugaban da mukarrabansa.

Jim kadan bayan haka, wani gidan Rediyon Habasha yayi zargin cewa an kashe Tafari da mukarrabansa saboda magoya bayan EPRP ne a asirce. Mengistu ya yi ikirarin cewa ya gano wani tsari mai shafuka 47 a hannun Tafari, wanda ya yi cikakken bayani kan yadda EPRP za ta maye gurbin mulkin gurguzanci a kasar.

 

7. Anwar Sadat, Egypt

A ranar Talata 6 ga Oktoba, 1981, Anwar ya halarci faretin nasara da aka gudanar a babban birnin Masar, sojoji shida na wani rukunin tankokin yaki sun yi amfani da faretin sojojin na tunawa da yakin Oktoba 1973 don kai farmaki kan shugaban ƙasar da gurneti da bindigogi. Nan shugaban kasar Anwar ya samu Mummunan rauni, bayan yan a wanni da samun raunin Allah ya karbi rayuwarsa. Harin na zuwa ne ‘yan makonni bayan babban harin da shugaban na Masar ya kaddamar kan masu tsassauran ra’ayi kishin addinin Islama, inda ake zargin su suka kai masa harin. 1981

 

8- Ahmed Abdallah, comoros

A ranar 25 ga Oktoba, Abdallah ya karbi mukamin shugaban kasa a comoros kuma ya ci gaba da zama a kan mukaminsa har zuwa rasuwarsa, duk da anyi masa yunkurin juyin mulki har sau uku ba’a samu Nasara ba.

A ranar 26 ga Nuwamban 1989, an harbe Ahmed Abdallah a ofishinsa na Moroni a kan wani yanayi da ake takaddama akai. Kowa yana zargin cewa wani da ake kira Denard shi ya kashe Abdallah, saboda ya ɗaure shi sannan ya sauke shi a matsayin kwamandan tsaron fadar shugaban ƙasa. Bisa wannan zargin an kai Denard kotu a birnin Paris da ke kasar Faransa a 1999. Daga karshe an wake Denard saboda rashin ingantaccen shaida.

 

9. Cyprien Ntaryamira

Watan Janairu 1994 Majalisar Dokoki na kasar Burundi ta zaɓe Ntaryamira a matsayin Shugaban Burundi

A ranar 6 April 1994 a misalin karfe 8:23 na dare, a yayin da jirgin sama da ke dauke da shugaban kasa Ntaryamira ke gab da isa filin jirgin sama na Kigali , nan wasu mutane suka harbawa jirgin da shugaban ke ciki makamai masu linzami biyu, inda makami mai linzami na biyu ya samu jirmu jirgin. Wannan hadarin shi yayi sanadiyyar mutuwar dukkan wadanda ke cikin jirgin. Har zuwa yanzu ba’a ba’a gano wa’yanda suka hallaka shugan kasar ba.

 

10. Ibrahim bare mainasar, Niger

bare mainasar ya hau kan karagar mulkin kasar Niger a ranar 27 Janairu 1996.

A ranar 9 ga Afrilu, 1999, sojoji sun yi wa Maïnassara kwanton bauna suka harbe shi har lahira a filin jirgin sama da ke Yamai babban birnin kasar yayin da zai hau jirgi mai saukar ungulu da ke kokarin tserewa da shi daga kasar. An kashe Kanal Bare ne a wani kokarin juyin mulki da masu tsaron lafiyarsa suka aiwatar, inda Manjo Daouda Malam Wanke ya karbi shugabancin kasar.

Daga nan yayi sauye sauye kan kundin sarin mulki ta kasar Niger din.

Ku bude bidiyon da ke kasa domin kallon na sauran kamar su Gaddafi, Murtala, idris deby da dai sauran su.

Kalli a bidiyo 👇👇👇

Mungode daga AREWA WEB

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!