LABARAI

Bidiyo | Yaro mai shekaru 15 ya kawo abokinsa domin ayi tsafi da shi ya samu kudi.

Wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta ya nuna wani yaro dan shekara 15 yana gabatar da abokinsa ga wani masafi domin a kashe abokin nasa ayi subbu da shi ya samu kudi.

Kafofin yada labaran Najeriya sun rawaito cewa yaran ‘yan makarantar sakandare ne da ke zaune a Najeriya kuma aminai ne. Ana ganin matashin wanda yazo sadaukar da abokin nasa yana gaya wa masafin cewa yana so ya sadaukar da abokinsa don ayi tsafi da shi ya samu kudi yayin da shi kuma wanda aka so a sadaukar yana rokon su, sannan kuma ya tunatar da abokinsa cewa shi kaɗai ne a wajen iyayensa.

Duk da haka, yaron ya ƙi ya saurare shi kuma lokacin da masafin ya tambaye shi ko yana so ya fille kan abokinsa idan aka ba shi wuka, ya ce zai yi.

Haka kuma a cikin faifan bidiyon, da aka tambaye shi ko wace mota ce yake son tukawa, ya ce yana shirin siyan mota kirar Mercedes GLK idan ya samu arziƙi ta hanyar tsafi. Shi kuwa abokin nasa wanda aka zo sadaukarwa ya ci gaba da rokon abokinsa hakan yasa masafin ya tambayi dalilin da ya sa ya zo wurin matsafin idan baya so ya mutu, Wanda abin ya shafa ya amsa da cewa abokin nasa ne ya nemi ya raka shi ba tare da tsammanin komai ba sai ya bi shi.

Bidiyon ya girgiza masu amfani da yanar gizo kuma hakan yasa mutane sun tattaunawa game da haɗarin da matasan yanzu ke ciki, na son yin kudi ko ta halin kaka.

Kalli bidiyon nasu a kasa amma ba a yaren hausa suke magana ba 👇👇👇

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!