TATTAUNAWA

Tattaunawa da Maryam Yahaya akan rayuwar da yadda ta shigo film.

Tarihin maryam yahaya

TAKAITACCEN TARIHIN KI?

Sunana maryam Yahaya an haife ni a unguwar Goron-Dutse, nayi primary school dina a Yelwa Primary School sannan nayi secondary school a Janguza.

YA AKA YI KIKA FARA FILM

Tun ina karama ina da sha’awan Film kuma har Allah ya cika min burina, ina farin ciki sosai, ban san irin farin ciki da nake ba, ina kara godewa Allah.

 

A WACCE SHEKARA KIKA FARA FILM?

Na shigo masana’antar kannywood a 2016, na fara fitowa ne a film din Mansoor.

KIN YI FINAFINAI SUN KAI NAWA?

Ban san adadin finafinan da nayi ba.

A CIKIN FINAFINAN DA KIKA YI WANNE FILM KIKA FI SO?

Duk finafinan da nayi ina son su, saboda duk film din da na fito a ciki, na fito ne saboda ina son shi.

WANNE FILM NE YA FI BAKI WAHALA?

Film din da nafi shan wahala sosai a cikin sa shine film din MARIYA, Don akwai wani faduwa da nayi a ciki naji ciwo sosai.

ME YAKE SA KI FARIN CIKI?

Abinda yake sa ni farin ciki shine naga iyaye na da yan uwa na suna farin ciki.

ME YAKE SA KI BAKIN CIKI?

Abinda yake sa ni bakin ciki shine idan na tuno watarana zan mutu na koma ga Ubangiji na.

WANNE IRIN ABINCI KIKA FI SO?

Nafi son Tuwo da miyan Kubewa.

WACE CE BEST FRIEND DINKI A KANNYWOOD?

Bani da best friend a kannywood, best friend dina ita ce mama t, a kannywood ina da iyaye, kanne da yayye.

WACCE TAMBAYA AKA FI YI MIKI?

Anfi yi min tambaya ne akan finafinan da nake yi.

WACCE AMSA KIKE BA SU?

Daidai da tambayar da suka min.

WADANNE KASASHE KIKA TABA ZUWA?

Naje saudiyya, dubai, gambia, Niger da dai sauransu.

WACE KASA KIKE FATAN ZUWA?

America

WACE KASA KIKA FI DADIN ZUWA ?

Babu kasar da nafi dadin zuwa kamar kasar Saudiyya.

MENENE BABBAN FATANKI A KANNYWOOD?

Na rabu da kowa lafiya a kannywood sannan naje nayi aure.

A BAYA AN DAINA GANINKI A KANNYWOOD?

Rashin lafiya nayi shi ya sa.

SHIN KINA SIYASA?

Eh ina yi.

MUN GODE DA TATTAUNAWA DA KIKA YI DA MU.

Kalli tattaunawar a bidiyo 👇👇

 

Nima Nagode.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!