TATTAUNAWA

Tattaunawa da sabira gidan bamadasi akan rayuwar ta da baku sani ba, da yadda ta shigo film

Tarihin sabira gidan badamasi yar auta

TAKAITACCEN TARIHIN RAYUWAR KI?

Sunana Hauwa Garba an fi sani da Yar Auta ko kuma Sabira na Gidan badamasi, An haife ni a garin Bici local government sannan anan nayi primary school dina daga nan aka min auren fari da yake ni bafulatana ce.

AUREN KI NAWA ZUWA YANZU A RAYUWAR KI?

Nayi aure sau uku a rayuwa ta.

YA’YANKI NAWA?

‘ya’ya na biyu amma daya ya rasu.

KIN TABA YIN SAURAYI A KANNYWOOD?

A’a amma na taba yin miji a kannywood, na auri Rabilu Musa dan Ibro, a aure shi shekaru 16 da suka gabata kuma na haifi yaro guda a gidan sa mai suna Muhammadu Arfat amma yanzu yaron ya rasu.

AINA KUKA HADU DA IBRO HAR YA AURE KI?

Ya aure ni a garin Kano a sokoto road, na hadu da shi a lokacin da yazo yin drama garin mu, anan ya kalle ni yace yana so na, kuma Allah ya ƙaddari aure na da shi.

KUN ZAUNA SHEKARU NAWA DA SHI IBRO?

Shekaru biyu muka yi a tare.

ZAKI IYA FADA MANA ABIN DA YASA KU KA RABU?

Kaddara ce kawai ta raba mu, kuma har ya rasu ina son shi yana so na.

MATAN SA NAWA KIKA ZAUNA DA SU?

Na zauna da matan sa uku, kuma ni ce ta Hudu.

KI DAN BAYYANA MANA YADDA RABILU MUSA DAN IBRO YAKE A LOKACIN DA YAKE MIJIN KI?

A maganar gaskiya Ibro bai da matsala, kawai Allah ne ya kawo zamu rabu, domin komai mace take so yana mata, tufafi, abinci da komai idan kina bukata zai baki.

BAYAN KUN RABU, KUN TABA FITOWA A FILM GUDA KUWA?

A’a bai yarda mun fito a film guda ba, nima ban yarda mun fito a film guda ba.

YA AKA YI KIKA SHIGA KANNYWOOD?

Tun kafin na shiga film ina wasan Drama irin na unguwa, watarana sai jarumi Dan Auta, Baba Ari da Musa mai sana’a da marigayi cinnaka suka zo katsina sai na hadu da su, suka ce min nazo na shiga film.

KIN FITO A FINAFINAI SUN KAI NAWA ?

Gaskiya ban sani ba amma suna da yawa.

KIN YI SHEKARU NAWA A MATSANA’ANTAR KANNYWOOD?

Na kai shekaru 14 zuwa 15 a kannywood.

A WANI FILM KIKA FARA YIN SUNA?

Film din Yan Uku-Uku, da kuma film din Bita Zaizai.

WADANNE NASARORI KIKA SAMU A HARKAR FILM?

Nasara na farko shi ne yadda jama’a suke so na maza da mata, kowa ya hadu da ni so yake ya gaisa da ni wannan ma babban nasara ne, sannan kyaututtuka da ake bamu shi ma babban nasara ne.

WANI ROLE KIKE TAKAWA A SERIES DIN GIDAN BADAMASI?

Duk abinda nayi a film din Gidan Bamasi ya birge ni, kuma a film din ni bana son a cuci Alhaji saboda tun ina yarinya ina tare da shi har na girma.

A CIKIN JARUMAN GIDAN BADAMASI, ROLE DIN WANI JARUMI NE YAFI BIRGE KI?

Ai duk jaruman film din suna birge ni, musamman Taska.

ME YAKE SAKA KI FUSHI?

Abinda yake saka ni fushi, shi ne ban yi abu ba ace nayi.

SHEKARUN KI NAWA DA HAIFUWA?

Shekaru na 39

Kalli tattaunawar a bidiyo 👇👇

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!