SHARHI

Kalli jerin matan kannywood mata da suka shigo film bayan sun fito a gidan mazajen su.

Wasu na ganin cewar da zarar jaruma ta yi aure shikenan tauraronta ya daina haske a masana’antar, amma Arewa web ta yi duba a kan wasu jarumai biyar da suka shahara bayan sun rabu da mazajensu.

Danna nan domin shiga kungiyar mu WhatsApp danna nan.

1.Jamila Nagudu

Jaruma Jamila Nagudu, ta yi fice sosai a fina-finan Kannywood, ta yi fina-finai da dama, amma kafin shiga harkar Kannywood ta taba yin aure har da yaro guda.

Jamila ta fito a fina-finai da dama amma wanda ta fi taka muhimmiyar rawa a ciki kuma wanda ya zama shi ne silar daukakarta shi ne fim din ‘Jamila da Jamilu’, wanda ta fito tare da jarumi Ibrahim Maishinku a shekara ta 2008.

2. Hafsat Idris

Hafsat Idris ta yi fice a masana’antar shirya fina-finai ta Hausa, bayan ta rabu da mijinta Alhaji Kabir, wanda suka haifi yara biyar da shi.

Jarumar ta fara fitowa a cikin fim din ‘Barauniya’ wanda da shi ne wasu ’yan kallo ke kiranta da shi.

Tuni Hafsat ta zama daya daga cikin manyan jarumai mata kuma masu shirya fina-finai da ake damawa da su a masana’antar Kannywood.

Danna nan domin shiga kungiyar mu WhatsApp danna nan.

3.Umma Shehu

Umma Shehu na daya daga cikin jarumai mata fitattu a Kannywood kuma cikin wa’yanda suke haskawa a duniyar kannywood.

Amma kafin shigarta masana’antar kannywood jarumar ta taba yin aure, inda ta ke da ‘ya’ya mata guda biyu.

Ta fito a fina-finai irinsu Mijin Badariyya, Bakon Yanayi, Amaryar Kauye, Burin So, da kuma shiri mai dogon zango na arewa24 Gidan Badamasi.

 

4. Momee Gombe

Bayan rabuwarta da mawaki Adamu Fasaha, momee Gombe ta tsunduma cikin harkokin wakoki a masana’antar Kannywood wcce ta yi fice a cikin wakar ‘Jaruma’ ta mawaki Hamisu Breaker.

Bayan tauraronta ya haska a fagen waka, jarumar ta fara fitowa a cikin fina-finai kamar su Zainabu Abu, Manyan Mata, Gidan Danja da sauransu.

 

5. Aisha Najamu

Binciken Arewa web ya gano jarumar ta taba yin aure har da yara biyu kafin ta shigo masana’antar Kannywood.

Jarumar ta yi fice a cikin shirin fim mai dogon zango na lawal Ahmad na Izzar So wanda a cikinsa ne ta nuna bajinta har tauraruwarta ta haska, aka fara damawa da ita a cikin masana’antar ta kannywood.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!