LABARAI

“Naso ya zauna amma Yaki” : Nico González (dan wasan kollon Barcelona)

Ina so ya zauna amma ya dage ya ci gaba da neman karin lokacin wasa, “in ji Xavi Hernandez a wani taron manema labarai ranar Juma’a game da Nico Gomzalez.

Kuma a wannan Asabar din, washegarin wannan sanarwar, Barça ta sanar da tsawaita kwantiragin matashin dan wasan tsakiyar.

“FC Barcelona da dan wasan Nico González sun cimma yarjejeniya kan tsawaita kwantiragin dan wasan wanda zai kare a ranar 30 ga Yuni, 2024, har zuwa 30 ga Yuni, 2026. Kundin sakinsa ya kai Yuro biliyan 1. Inji sanarwar da ta fito daga Barcelona.

An rence shi (Nico González) a tawagar da Gennaro Gattuso ke jagoranta. “Daga baya, Barça da Valencia sun cimma yarjejeniya game da rancen dan wasan na kakar 2022/23, ba tare da zabin siya ba.”

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!