TATTAUNAWA

Tattaunawa da Daddy hikima akan rayuwarsa da baku sani ba.

Tarihin daddy hikima abale

TAKAITACCEN TARIHIN KA?

Sunana na yanka Adam Abdullahi Adam wanda aka fi sani da a Abale sannan ana kirana da Daddy hikima an haife ni a garin kano.

YA AKA YI KA SHIGA MATSANA’ANTAR KANNYWOOD?

A farko dai ban shigo kannywood a matsayin Actor ba, na shigo ne a matsayin designer, amma ni burina na so na zama director.

ME KA KARANTA A MAKARANTA?

Na karanci kiwon lafiya, ni nurse ne.

AINA KAKE AIKI?

Ina aiki a asibiti, amma saboda yawan ayyuka da nake da su a kannywood, sai da kawai ina zuwa watarana domin taimako.

KANA DA AURE?

A’a bani da aure, In Allah ya kawo ranara za’a yi, aure da mutuwa duk na Allah duk ranar da yace zaka yi to sai kayi shi.

KANA DA BUDURWA?

Eh, ina da shi, kuma inch’Allah idan muka shi aure zan gayyace ku.

AN TABA MAKA WANI KYAU DA KAJI DADI SOSAI?

Eh, kyautar mota da rarara ya bani, naji dadin sa sosai.

MENENE BABBAN BURUNKI?

Watarana na zama soja shi yasa na shiga nurse, nina son soja sosai.

WANNE ABINCI KAFI SO?

Kayan ciki, ina son kayan ciki da ganda

WACE CE GWANAR KA A KANNYWOOD?

Aisha Aliyu Tsamiya

MUN GODE DA TATTAUNAWA DA KAYI DA MU.

Nima na gode.

 

Tattaunawa da sabira gidan bamadasi akan rayuwar ta da baku sani ba, da yadda ta shigo film

Tattaunawa da sabira gidan bamadasi akan rayuwar ta da baku sani ba, da yadda ta shigo film

Tattaunawa da sabira gidan bamadasi akan rayuwar ta da baku sani ba, da yadda ta shigo film

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!