LABARAI

Yadda akayi wa wasu sojoji 7 kisan gilla a Kamaru

Sojojin gwamnatin Kamaru bakwai ne aka kashe a safiyar Laraba, 10 ga watan Agusta, 2022, a hannun Ambazonia Restoration Forces(Yan tawaye) a garin Bamboutos, wani yanki da ke yammacin kasar Kamaru.

Al’amarin da ke kara ta’azzara. Bamboutos ya kasance a yankin yammacin kasar(Kamaru) mai iyaka da yankin masu magana da harshen Ingilishi( English) n’a arewa maso yamma mai fama da tashe tashen hankula tun farkon rikicin, wannan yankin ya sha fama da hare-haren ‘yan aware shekaru biyar da suka gabata. Wanda Harin na yau shi ne na shida.

Rikicin ‘yan aware da makami ya addabi yankuna biyu na Arewa maso Yamma da Kudu maso Yamma masu magana da Ingilishi tun daga shekarar 2016, inda kungiyoyi masu zaman kansu da Majalisar Dinkin Duniya ke zargin ‘yan aware da sojojin gwamnati akai-akai game da laifuffukan da ake yi wa farar hula.

Ya zuwa yanzu, an kashe a kalla sama da mutane 3,000 tun farkon rikicin. Inda kuma sama da mutane miliyan daya suka rasa muhallansu. da kuma sauran masu neman mafaka a kasashen da ke kusa, musamman Najeriya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!