SHARHI

Kalli motocin jaruman kannywood mata da babu mai tsadar su duk kannywood.

 

Motar HAFSAT IDRIS

Jaruma a Hausa film ta bawa masana’antar mamaki jim kadan bayan aurar da babbar yarta da tayi, Jaruma Hafsat Idris wanda akema lakabi da Hafsat barauniya ta sayi mota kirar formatic ta kimanin naira Miliyan goma sha bakwai, wannan lamari ya girgiza masana’antar da abokan aikinta matuka. 

Hafsat idirs ta wallafa karin arziki da tayi na sayan motar ne a shafinta na Instagram inda dimbin masoyanta da abokai suka rinka yimata fatan alheri da addu’a ta alheri, yayinda abokan harkarta da dama suka rinka wallafawa suma a shafikansu don tayata murna ciki harda sarki Ali nuhu wanda mutane da dama sukeyi masa kallon amini, mai gida kuma aboki na kut da kut ga Hafsat idris.

Ita dai hafsat idris ta taba aure kuma tanada yara da dama kuma lallai kyakykyawace matuka duk da cewa ta taba aure, tanada dimbin masoya da dama tareda mabiya masu yawa kuma jigo ce a harkar film na hausa inda ta taka rawa a manya manyan finafinai da ake Ji dasu kamarsu labarina na aminu saira wanda ake sanyawa a tashar arewa 24 da ma sauran fina finan hausa masu tasiri matuka.

 

Motar HADIZA GABON

Tauraruwar masana’antar fina-finan hausa ta kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta samu abun farin ciki inda aka yi mata kyautar mota.

Jarumar ta samu kyautar motar kerar Honda daga aminiyar ta, Laila Ali Usman , wacce take shugabantar kamfanin L and N interiors.

Tauraruwar ta sanar da labarin mai farantar da rai a shafin ta na instagram tare da rubuta sako na mika godiya.

Ta rubuta “thank you madam kudi ,my new car @landninteriors thank u”.

 

Motar FATI WASHA

Tauraruwar fina-finan Hausa, Fati Washa ta yi sabuwar mota kirar Toyota kamar yanda abokin aikinta, Nasir Ali Koki ya saka hotunan motar ya kuma taya jarumar murna. Fati washa dai tana daya daga cikin jaruman kannywood da basu taba yin aure ba, tabbas tana daya daga cikin jaruman kannywood mata masu tashe da kyaun gaske.

 

Motar Jamila NAGUDU

 

Shahararren mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara ya Bawa jarumar Kannywood Jamila sabuwar mota kyauta – ƙirar Toyota Matrix – Dama dai Rarara ya saba yiwa abokan sana’ar tasa sha tara ta arziki lokaci zuwa lokaci Fitaccen mawakin nan na siyasa kuma Shugaban mawakan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Dauda Kahutu Rarara

Lokuta da dama, su kan fito su nuna jinjina da yabawa a kan wani abun azo a gani da yayi musu a shafukansu na zumunta. A wani bidiyo da aka wallafa a shafin real_rarara_multimedia ta Instagram, an gano jaruma Jamila Nagudu cike da farin ciki da murna a lokacin da Rarara ke mika mata mukullin motar da ya mallaka mata. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!