KANNYWOOD

Bidiyo | an samu wani mai kama da Ali Nuhu kamar am tsaga kara a indiya kalli bidiyon

Kalli a bidiyo 👇👇👇

An samu wani ba’indiya mai kama da babban jarumin kannywood wato Ali Nuhu, wannan labari ne da wasu suka ringa yaɗa shi a social media, mutane da yawa sun yi mamakin kallan wannan bidiyon, a yayin da wasu kuma basu yi mamakin hakan ba, saboda ansha samun wasu mutane da suke kama da wasu mutanen kamar an tsaga kara.

Shin da gaske ne an samu mai kama da jarumi Ali Nuhu a India? Kamin mu amsa muku wannan tambayar bari Ku kalli bidiyon wanda aka ce yana kama da jarumi Ali Nuhu.

Bayan kallon wannan bidiyon gaskiya24 ta fara bincike akan wannan bidiyon domin ta dan fara tantama akai saboda kwanakin baya an fidda wani bidiyo makamancin wannan na jaruma A’isha humaira da Maryam booth.

A bincike da wannan tashar ta gaskiya24 tv tayi ta gano cewa wannan Kama ba na gaske bane, anyi amfani ne da wani sabon manhajar Android mai sun reface aka canja a salin fuskar jarumi da ke kan bidiyo mai suna hrithik Roshan aka sanya na Ali Nuhu, hakan na yi’uwa da sabon manhajar da ka kirkiro mai suna reface, Ku kalli asalin fuskar da ke kan bidiyon.

a takaice dai wannan Kama ba ta gaske ba ne. Kirkirarren abu ne. Ga mai son wannan manhajar ko kuma ince application ya dannan description da ke kasar wannan bidiyon zai ga link sai ya Danna zai ga inda za’a saukar da wannan bidiyon.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!