SHARHI

Jaruman kannywood mata 5 da suka fi iya Rawa a kannywood da aka tantance a 2022

 

1- RAHAMA SADAU

Rahama Sadau itace jarumar datake da shahararren kamfanin shirya fina finai na sadau pictures Wanda yake gudanarda kasaitattun fina finan da a tarihin kannywood baza,a manta dasuba.

Rahama babbar jaruma ce a kannywood da kuma Nollywood wata finafinan kudancin Nigeria, ta kasance manyan jaruman kannywood mata da suke da kudi sosai, jarumar ta koyi rawa ne tun kafin shigowarta kannywood, hasalima Jarumi Ali Nuhu a wajen rawa ya fara ganinta, sannan ya jawo hankalinta domin ta shigo harkokin finafinai na Hausa, tabbas duk mai bibiyar harkokin finafinan kannywood yasan wannan jaruma ta iya rawa, shi yasa tayi nasara ta zamanto a na daya cikin jaruman kannywood mata da suka fi iya rawa.

2- RAKIYA MUSA

rakiya Musa wacce wasu ke kiranta da A’isha, sunan A’isha humaira ya samo asali a wani Film da ta fito tare da jarumi adam a zango mai suna A’isha humaira, jarumar haifaffiyar kasar Nijar ana yawan ganinta a bidiyoyin wakokin Hausa tare da mawaka kamar garzali miko, HAMISU BREAKER da sauran su, tabbas jarumar rakiya, mutane na yabon irin rawar da take takawa a irin wa’yannannan wakokin na bidiyo kuma ta iya sosai, shi yasa tayi nasara ta zamanto a na biyu cikin matan kannywood da suka fi iya rawa.

 

3- MARYAM YAHAYA

Jarumar kannywood Maryam mai shekaru 24 da haifuwa Anfara ganinta ne Acikin film din taraddadi. city people Entertainment sun bata award din jaruma mai nasara A shekarar 2017. Kuma Film din mansoor shi ya daga tauraruwarta sama. Matashiyar jarumar mai yayi, ta iya rawa sosai domin tafi da yawa daga cikin jarumai mata da suka dade suna taka rawa a masana’antar kannywood. Shi yasa tayi nasara ta zamanto a na 3.

 

4- AMAL UMAR 

Amal tana daga cikin matasan jaruman kannywood da ake ji da su a masana’antar, ita ma dai Amal ana yawan ganinta a bidiyoyin wakoki tana taka rawa, a binciken da muka yi mun gano cewa Amal ta cancanci ta zamanto a 4 cikin jaruman kannywood da suka iya rawa sosai.

 

5- NAFISA ABDULLAHI

An Haifi Nafisa Abdullahi a garin Jos a ranar 23 ga Watan Janairu 1993.Ta Yi Makarantar Firamare A Capital, Sannan Ta Wuce Sakandire Ta Dutse Dake Birnin Tarayya Da Ta Kammala A Shekarar 2007.

Nafisa Abdullahi Ta Fara Shiga Harkar Fim A Shekarar 2009. Ta Zama Jarumar Jarumai Ta 2013. Jarumar wacce yanzu haka tana digiri na biyu a fannin daukar hoto a London, ta iya taka rawa sosai wanda da yawan mutane sun shaida hakan. Shi yasa nayi nasara ta zamanto a na 5 cikin jerin jaruman kannywood mata wa’yanda suka fi iya rawa.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!