LABARAI

Gadar da ta hada Najeria da Bennin ta ruguje

Gadar kasa da kasa da ta hada Najeriya da jamhuriyar Benin a garin Chakanda dake karamar hukumar Baruten ta jihar Kwara ta ruguje, sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a tsakar daren jiya Lahadi, har zuwa yau litinin.

Gadar da ta ruguje wadda aka gina a shekarar 2010 a lokacin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Bukola Saraki, ta kasa shawo kan yawan ruwan da ya mamaye ta a lokacin da aka yi ruwan sama.

A halin da ake ciki kuma an dakatar da harkokin zamantakewa da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu a kan iyakar na wani dan lokaci.

Wasu daga cikin matafiya da suka zanta da jaridar ”Daily Sun” na son ganin kasashen biyu su shiga tsakani cikin gaggawa domin samun dorewar harkokin kasuwanci.

Da yake mayar da martani kan ci gaban, Sarkin Yashikira, Alhaji Umar Usman Seriki ya yi kira ga ma’aikatar ayyuka ta tarayya, Hukumar kula da tituna ta gwamnatin tarayya, FERMA da gwamnatin jihar Kwara su gaggauta kai dauki ga al’ummar yankin domin ganin an samar da mafita cikin gaggawa ga dgadar da ta ruguje.

Daya daga cikin mazauna garin Yashikira, Malam Lafia Gunu ya ce lamarin yana da matukar tayar da hankali domin a halin yanzu mahaifiyarsa Hajiya Halima Lafia da ta tafi jamhuriyar Benin ta makale a can sakamakon rugujewar gadar.
Ya roki Hukumomin da abin ya shafa su gaggauta fara gyaran gadar, ko kuma a samar da wata hanya ta daban da matafiya za su yi amfani da su musamman wadanda suke samun rayuwarsu ta yau da kullum ta wannan hanyar.

A nasa martani, Konturola na ayyuka na gwamnatin tarayya mai kula da kwara. Arewacin Najeriya, Injiniya Kayode Ibrahim ya bayyana cewa tuni mutanensa suka fara wata ziyarar gani da ido domin sanin irin barnar da aka yi da kuma samun mafita na wucin gadi. yayin da sakamakon ziyarar tasu zai tabbatar da matakin da za su dauka.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!