TATTAUNAWA
Trending

Tattaunawa da Kabiru nakongo akan rayuwar shi da zai baku mamaki da yadda ya shigo film.

Tarihin kabiru na kwango

KA GABATAR DA KANKA GA MASU KARATU?

Sunana Kabiru Abubakar Aliyu amma mutane sun fi sani na da Kabiru nakongo.

ZAKA IYA BAMU TAKAITACCEN TARIHIN KA?

An haife ni a shekarar 1962 kuma nayi karatu a hannun mahaifina sannan nayi karatu a wajen malam abu zan-zan daga nan naje makarantar koyan harshen larabci wato school for arabic studies, na dau tsawon lokaci har ya zamanto saura shekara daya kammala makarantar sai na bari nazo na fara karatun primary school daga shekarar 1974 zuwa 1980 na kammala primary school.

Sannan na tafi Makarantar secondary school kuma na kammala makarantar a shekarar 1985 tun kamin na kammala makarantar na yi aure, sannan a lokacin na sake yin exam a makarantar SAS nayi nasara, sannan nayi karatun NCI a shekarar 2001 zuwa shekarar 2004 a FCI Kano.

TAYAYA KA SHIGA HARKA FILM ?

Ina sha’awar yin Film tin ina karami, akwai actors irin su Kasim yero, mustapa Muhammad dan haki wa’yannan mutanen suna bani sha’awa, hakan yasa har nayi ta kokarin in shiga harkar film amma Allah bai sa ba, daga baya Allah ya bamu nasara har muka fara kirkiran kungiyoyin drama daban-daban a karshe dai mun kirkiri wata kungiya mai suna Sardau Use Grammatical Association wanda na zama fitacce a ciki, sai kuma nazo nakirkiri wata kungiya mai suna Dabo Film wanda ni na jagorance ta na tsawon lokaci kuma mun yi fina-finai da yawa a cikin ta.

FINA-FINAI NAWA KAYI A MASANA’ANTAR KANNYWOOD?

Ban san iya adadin films da nayi ba, saboda akwai wanda nayi a K7 na VSH wa’yanda basu fito kasuwa ba, amma film din da na fara fitowa a kannywood shine KILIU-TAJA-BAU daga nan na fara wasu finafinai.

ZAKA IYA TUNA DA FILMS DIN DA SUKA SAKA KA FICE?

Akwai fina-finai guda biyu wa’yanda suka sa nayi fice a cikin su sosai, akwai film din Linzami Da Wuta da kuma Film din Tawakkali wa’yanda suke negative sannan kuma nayi film din Akatsi wanda yake positive ne.

ME YAKE SAURIN BATA MAKA RAI?

Abinda yake saurin bata min rai shine naga ana iskanci akan titi, ko kuma naga mutum yana kokarin aikata rashin gaskiya kai tsaye da son zuciya, idan ka hadu da mutum sai kaga yana kokarin cutar ka, wannan shine yafi damu na.

WANI ABU NE YAFI SA KA FARIN CIKI?

Ina son naga ana Gaskiya a ko ina, kuma ina son jin yara su na karatun Alkur’ani.

MUN SAME KA A MAKARANTA MENENE MATSAYIN KA A WANNAN MAKARANTAR?

Ni jagora ne a makarantar.

YA BATUN IYALI ?

Ina da mata guda daya mai suna binta, mun haifi yara 12 a tare, sannan yaran mu 9 su na raye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!