LABARAI

Wata yar shekara 15 tayiwa kanta allurar HIV wato kanjamau

Wani matashi yana hannun ‘yan sanda bayan da aka gano cewa budurwarsa ‘yar shekara 15 ta yi wa kanta allurar jininsa mai dauke da cutar kanjamau a wani yunkuri na tabbatar da soyayyar ta a gare shi.

A cewar odditycentral.com, yarinyar ta fito ne daga kauyen Suwal Kuchchi da ke Assam a kasar Indiya, yayin da saurayin nata dan garin Hajo ne.

Shafin yada labarai ya ruwaito cewa saurayin ya yi kokarin guduwa da budurwar sa sau da yawa, amma sa idon iyayenta ya dakile yunkurin.

Bayan kusan shekaru uku suna soyayya, ba a sani ba ko saurayin yana shakkar soyayyar budurwarsa a gare shi bayan kokarin tserewa da ita bai yi nasara ba.

Sannan a kokarin tabbatar masa da soyayyar da ta ke yi masa, yarinyar ‘yar shekara 15, duk da sanin sarai cewa masoyinta na dauke da cutar kanjamau, sai ta zaro jininsa da sirinji ta yi wa kanta allura.

An bayyana cewa, iyayen yarinyar sun shigar da kara kan saurayin, lamarin da ya sa ‘yan sanda suka kama shi a Hajo, yayin da ‘yar tasu ke karkashin kula ta likitoci.

Saurayin zai iya kasancewa cikin matsala mai tsanani idan ya san shawarar budurwarsa ta yin abin da ta yi, ko ma ya amince da shi, ya san hadarin da zai haifar mata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!