LABARAI

Mahaifi ya bayyana dalilin da yasa yaringa saduwa da yarsa har suka haifi ‘ya’ya biyu a tare.

An kori wani mahaifi mai suna Amaechi Agnalasi da diyarsa daga cikin al’ummar Nnobi da ke jihar Anambra saboda saduwa da yaringa yi da yarsa har suka samu ‘ya’ya biyu a tare.

A cikin wani faifan bidiyo da wasu jama’ar unguwar suka dauka a yayin da ake yi wa mahaifin da diyarsa mai suna Queen Bassey ta fayyace cewa ita da mahaifinta ‘yan jihar Cross River ne.

A cewar Queen, mahaifinta Amaechi ya dauke budurcinta ne bayan matansa sun rabu da shi. Ta ce mahaifinta ya tilasta mata ta don ta zama matarsa. Amma cewarta bata san dalilin da yasa tabar dangantakar ta dade sosai ba.

Mahaifin, ya bayyana cewa yana lalata da ‘yarsa ne saboda ba ya son ta barshi kamar yadda matansa da sauran ‘ya’yansa suka yi. Ya kara da cewa ya aikata wannan abin kunya ne saboda saboda baya son ya daina ganinta a rayuwarsa.

An dai bayyana cewa, an kore su daga cikin al’umma ne saboda aikata irin wannan abin kunya da rashin sanin yakamata.

MunGode da karanta wannan labarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!