LABARAISHARHI

Jerin kasashe 10 da suka fi yawan yan damfara a duniya, Nigeria ita ce kasa ta 1

Damfara dai wani abu ne da kowa baya so a masa, bashi da bambanci da sata da kuma zamba cikin aminci.

Kasashe da yawa a duniya suna fuskantar matsalar yan damfara inda wani takanas ta kano zai yi yaje wani kasar domin damfara.

An tantance kasashe 10 da suka yawan yan damfara a duniya kalle su a wannan bidiyon na kasa.

Ba abin mamaki bane dan kun kalli Nigeria da ta kasance a matsayin ta daya cikin kasashe 10 da suka fi yawan yan damfara a duniya.

Domin a Nigeria mutum zai kiraka a waya yace shi aljani ne zai baka magani amma ka turo masa kudade daga nan sai yayi blocking dinka da sauran hanyoyi damfara dai, wanda da za’a bawa kowa dama da zai kawo hanyoyin da yan damfarar Nigeria ke amfani da shi wajen damfara da baza su irgu ba.

Allah ya kawo mana saukin wannan al’amarin a wannan kasar tamu ta Nigeria.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!