SHARHI

Bayanin kan jaruman kannywood da suka rasu a 2021 da kuma cutar da ya kashe kowa daga cikin su.

1: SANI GARBA SK

sani garba sk ya kasace jarumi ne wanda yadau shekaru da dama ana damawa dashi a masanantar kannywood,kafin shigarshi masanaantar kannywood ya kasance mawaki mai yabon manzon Allah SAW.

Sani yayi fama da rashin lafiya na tsawon shekaru 3, a baya kafin rasuwarsa ya fito ya nemi taimakon jama’a kan rashin lafiya da yake fama dashi a lokacin anyi ta yada labaran karya wai ya mutu ,inda shi da kanshi ya fito ya karyata labaran mutuwar tasa , daga lokacin bai wuce watanni biyu ba Allah ya karbi rayuwarsa. Sani sk ya rasu a ranar 15 ga watan disemban shekarar 2021 ya rasune a sanadiyar ciwon suga da ya haifar masa da ciwon hanta da na koda.

2: ZAINAB BOOTH

zainab booth ta kasance tsohuwar jarumar kannywood da suka goya masanaantar tun tana yar jaririya , a kwanakin baya ne dai kamin rasuwarta marigayiya tayi fama da rashin lafiya lamarin da ya kai har anyi mata aiki a kwakwalwa, kamar yadda yayarta maryam booth ta dinga wallafa hotunan a shafukan sada zumunta.

Margayiyar takasance daya daga cikin taurarin kannywood da yayunta uku suka kasance suma taurari, ta rasu ne birnin kano a daren alhamis , ran 2 ga watan 7 shekarar 2021, Allah ya karbi rayuwarta tanada shekaru 61 a duniya , ta rasu ta bar yaya 4, maza 2 mata 2, wato umar,sai amude da maryam dakuma sadiya, sai jikoki guda 2. ita dai margayiyar zainab booth an bayya cewa ciwon kwakwalwa da tayi ta fama dashi shi yayi sanadiyar rasuwarta.

3: AHMAD TAGE

jarumin barkwanci kuma dadden mai daukar hoton bidiyo wato cameraman a kannywood , malam ahamad aliyu tage yarasu ran 13 ga watan septembern 2021 , Allah ya karbi ransa yanada kimanin shekaru 55 a duniya , kuma yabar yaya 21 da matansa na aure guda 2, dimbin mutane ciki harda abokan sanaarsa yan fim sun halarci jana’izarsa wanda aka gudanar a gidansa dake unguwar sheka karshen kwalta.

Dan uwan marigayin ahmad mai suna umar ya bayyana cewa marigayin ya sanar dashi cewa wannan cutar ba ta tashi bace, yake cewa in ya mutu a yafe masa. tage ya rasu ne a asibiti a kano bayan yayi jinyar ciwon bugun zuciya da ya samu.

4: ISIYAKU FOREST

Mawakin siyasa isiyaku forest yana daya daga cikin mawakan da sukayiwa shugaban kasa muhammadu buhari wakoki a lokacin yakin neman zabe fitaciyar wakar da forest yafito a cikin ta itace wacce akayiwa buhari da jam’iya APC itace gaskiya dokin karfe wacce ta samu karbuwa a wajen masoyan jam’iyar gabanin zaben 2019, a shekarar 2020 .

An yanke wa forest kafa bayan tsawon lokaci da ya ,kwashe yana fama da rashin lafiya . A ranar 4 ga watan september 2021 forest ya rasu anji labarin cewa shugaban kasa muhammadu buhari ya turo da wata tawaga domin yiwa iyalan forest da yan uwa da abokan arziki ta’aziya.

5: HAJIYA BINTA TARAUNI

hajya binta tarauni wacce aka fi sani da kaka tabawa a cikin shiri mai dogon zango da tashar arewa24 take gabatarwa mai suna DADIN KOWA jarumar ta rasu ran 11 ga watan maris 2021 , hajiya binta dai ta bada gudunmawa ta hanyar fitowar ta da tayi a matsayin kakar wizi a shirin ta dadin kowa amma har yanzu ba’a bayyana ciwon da yayi sanadiyar mutuwar tata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!