KANNYWOOD

An kore su saboda bidiyon batsa amma ba’a kori maryam booth ba, shin kunsan dalili?

Kusan kowa a wannan duniyar baya son ace yau ga wani bidiyon shi na siraici ya bayyana musamman ga wa’yanda suke a arewacin Nigeriya a inda mutunci yafi komai. Hakan yasa hukumomin arewacin Nigeriyan suke hukunta duk wanda ya dauki bidiyonsa na tsiraici sannan ya yaɗa, amma shin me yasa aka ki hukunta maryam booth bayan bidiyonta ya bayana.

 

Maryam Hiyana.

A shekarun baya Jaruman kannywood ta farko da bidiyon tsiraicin ya fara bayyana a duniya itace maryam hiyana.

Bobo Dan canji shi ne wanda ya dauki bidiyo sannan ta hanyar bidiyon ya yadu, daga baya ya gudu yaje ya buya sannan itama Jarumar a lokacin sai da ta ɓuya saboda jami’an musulunci na hisba sun fara neman ta ruwa a jallo. Tun daga wannan lokacin aka fara yi wa yan kannywood kallon mutanen banza.

A wannan yanayin aka sanar da korinta a matsana’antar kannywood tare da wasu jaruman kannywood din mata da ka yi zargin sune suka yi tsilar ya duwar bidiyon nata.

Daga karshe sai hawayen nadama ya kwararo a idanun Maryam Hiyana.

Tun daga nan ta fada azuci, ta sanar afili cewa ta tuba Allah ya gafarta mata.

Kuma taba masoyanta hakuri cewa: idan Allah yaso ba zata kuma aikata laifi irin wannan ba.

Inda daga karshe wani daga cikin masoyanta ya aureta har ta samu ‘ya’yan 5 da mijin da shi.

A wancan lokacin dalilin da yasa aka kori maryam hiyana daga matsana’antar film shine, wannan bidiyon da aka yi da ita, da sanin ta aka yi shi sannan ba tirsasata aka yi ba, shine tsilar korinta da yasa aka yi.

Safeeyah yusuf , Safara’u.

Safeeyah yusuf wacce aka fi sani da Safara’u, ta samo wannan sunan Safara’u ne a wani shirin mai dogon zango ta tashar arewa 24 suke gabatarwa mai suna Kwana Casa’in, a shirin an bayyana a matsayin nisassiyar yarinyar mai tarbiya wacce ya kamata ta zamanto abar koyi a idanun jama’a.

Watarana sai aka wayi gari aka ga bidiyon ta na siyarci yana yaduwa a social media, wanda hakan yasa hukumar Moppan ta koreta a kannywood sannan su ma Arewa24 suka daina haskata a shirin su na kwana Casa’in.

A wannan lokacin jaruman ta shiga mawuyacin hali a yadda ta bayyana ko fita bata iya yi a gida sannan ta kara irin wannan bidiyo nata da aka gani yana yawo kusan ko wacce daga cikin yan matan yanzu tana da shi a wayar ta.

Maimako aga ta tuba ta fito ta bayyana nadama akan wannan bidiyon nata na batsa sai aka ganta tare da wani mawaki wai mr422 suna wakar batsa a tare, hakan yasa mutane suka ci gaba da yi mata kallon ballagaza.

Ita dai babbar hujjar da ya sa aka kore ta shine wannan bidiyonta da aka ga ya bayyana a duniya, ita ce ta dauki bidiyon da kanta sannan wasu na cewa saurayin ta turawa kamar yadda tace wasu suna fada a hirar da aka yi da ita a gidan bbc, ita da ake mata kallon kamila abar koyi a shirin kwana Casa’in ace tayi irin wannan abin kunya.

Maryam Booth 

Jarumar kannywood maryam booth ta kasance jaruma ce a kannywood tun tana karamar yarinyar kasancewar mahaifiyarta marigayiya zainab booth Allah yajikanta da rahama tsohuwar jaruma ce a kannywood, watarana an wayi gari anga wani bidiyon tsiraicinta da aka dauka yana yawo a shafukan sada zumunci.

kunsan mutanen idan suka samu irin wannan abin sai su yi ta yaɗawa a social media, nan da nan kowa yasan labarina abinda ya faru, jarumar bata yi kasa a gwiwa ba wajen fitowa ta bayyana yadda bidiyo ya fito da yake bidiyon anga wani yana daukar ka da bidiyo alhalin tana tsirara da ta lura ana daukarta tayi maza taje ta dakatar da daukar.

A bayanin ta tace wata kawar ta ce ta dauke ta a bidiyon kuma da ta lura tana daukar ta a bidiyon sai tayi maza taje ta kwaci wayar ta ta sannan ta goge bidiyon ashe ita ta manta a iPhone idan ka goge video za’a iya kuma da dawo da ita. Tambayar da mutane suka dinga yi a lokacin shine, shin me yasa ta bayyana tsiyarcin ta a gaban kawarta?

Ana wannan yanayin ne sai aka ji labarin takai karar mawaki Deezell kotu kan zargin ya yaɗa bidiyon ta na batsa. Sannan wasu sun ce tsohon saurayin ta ne. Ko ma dai menene, dalilin da yasa ita ba’a kore ta ba shine: wannan bidiyon da ya fito ba itace ta dauke shi ba sannan ba da sanin ta aka dauka ba hasali ma cin amanar ta aka yi, sabanin sauran da kansu suka dauki bidiyo ko da sanin su suka bari aka dauki bidiyon nasu, Hakan shi yasa ba’a kore ta a kannywood ba.

One Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!