KANNYWOOD

Innalillahi wa’inna ilaihi rajium, Allah yayi wa jarumin barkwanci Sa’adu ado (ƁAWO) rasuwa a yau, Allah yajikanshi da rahama

Innalillahi Wainna ilaihirrajiun Allah yayiwa Jarumin Barkwanci SA’ADU ADO GANO Wanda akafi sani da (ƁAWO) rasuwa, kuma tuni akayi janaizarsa kamar yadda Addinin Musulunci ya tanadar.

 

Bawo dai yana daya daga cikin Manyan Jaruman Barkwanci wanda suke gudanar da harkokinsu na wasan barkwanci tare da marigayi rabilu musa ibro

 

Ya kwashe shekaru da dama yana wannan Harkar wanda kusan suna cikin zubin farko farko da marigayi rabilu musa ibro ya fara dasu, Film dinsu na karshe da marigayin shine fim din karangiya wanda akayishi a babban Birnin tarayya abuja tare da wasu Fitattun Jaruman kudancin Nigeria.

Kamar Dai yadda aka sani a yanzu harkar Finafinan barkwanci taja baya matuka, Kasancewar yawancin jarumanta sun kwanta dama wanda a karshe kuma Jigon nata watau marigayi Rabilu Musa ibro Shima ya cimma sa’a

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!