LABARAI

Tattaunawa da Saratu Gidado (Hajiya Daso) akan rayuwar ta da zai baku matukar mamaki

 

Antaba marinki?

A’a ba’ataba marina ba gaskiya.

Kin taba cin tsiren tasha ?

Eeh nataba ci a lokacin ina yarinya karama, idan mahaifiyarmu zataje kauye damu, takan siya mana. a lokacin ne nataba ci.

Ya kikeji a lokacin ?

Dayake a lokacin yarintane , naji dadin shi sosai ma kuwa.

Zaki so ki kara tabawa ?

A’a gaskiya bazan so nakara tabawa ba

Wayar da Kika fara rikewa ?

Wayar da nafara rikewa ana ce mata Alcatel. wata kararramar waya.

Akwaita kuwa a yanzu ?

Eeh akwaita, domin na taba zuwa wani shago anan naganta

Kasar da kika taba zuwa ?

Kasar da nataba zuwa itace London

Kare ya taba binki ?

A’a kare baitaba bina ba, domin idan nazo wani gida kafin nashiga sai n’a tambaya da kare ko ba bu? idan da kare sai ankamashi zanshiga idan kuma ba bu sai nashiga kawai.

Wanne Kikafi tsoro ? Bera ko Kadangare ?

Nafi tsoron Kadangare, domin shi bera a kwai tarkon kamashi ai, amman Kadangare ba bu tarkon kamashi.

Minti nawa kike wajen kwalliya ?

Ina daukan lokaci mai tsawo wajen kwalliya domin na batar da tsufa na
ina daukan kamar awa daya da rabi wajen kwalliya.

Abin dake batamiki rai ?

Abin da ke batamin rai shi ne: cin mutunci, zaagi

Bazawarikin a Kannywood ?

Gaskiya ba ni da wani bazawari a Kannywood, domin ni gaba daya a matsayin yan uwa na daukesu.

Chatin ko waya ?

Agaskiya na fi son chatin, domin kana zaune ba sai kayi magana ba kawai rubutawa zakayi

Sirrin zaman aurenki ?

Sirrin zaman aurena shine jin dadi da walwala domin muna fahimtar junamun sosai iya gwadgwado ni da mijina

Sunan da kawayenki ke kiranki ?

Sunan da kawayena ke kirana shine: Saratu. Saboda dashi nayi makarantana da primary school har nagama.

Kina da wata baiwa ?

Eeh ina da wata baiwar da ban taba fadaba amma a yau zan fada. wato Allah ya bani baiwar da idan nayiwa mutum addu’a to inha Allahu tana karbuwa.

Darasin da mutane suka koya Miki a rayuwa ?

Babban darasin da nakoya a wajen mutana shine idan kayiwa mutum hallaci, sai yayi maka butulci. Bance dukkan mutane suke haka ba amma yawancin su haka suke.

Burodi ko gurasa ?

Agaskiya na fi son burodi saboda ya fi laushi. Domin gurasa tana da tauri, sai an yayyafa rura ko an ya ga kamin aci. Amma burodi shi soft ne

Saurayinki na farko ?

hahaha! ni da nake matsayin matar aure, bayadda za ayi nace gashi nan. Amma nasan yanan har yanzu

Zaki iya kwaikwayon mutane ?

Eeh zan iya kwaikwayon Kabiru Nakwango

A matsayin me kika dauki fim ?

Na dauki fim ni a matsayin business. domin idan muka ce fadakarwa muke, da zarar munyi kuskure, sai a dinga nunamu ana cewa su da sukace fadakarwa, ku kalli abin da sukeyi. Sabo da haka ni a matsayin business nadauki fim.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!