ILIMANTARWA

Yanzu, yan tijjaniya suka bukaci lallai a dawo da muqabalar da aka shirya da Dr idris dutsen tanshi.

Kwanakin baya gwamnatin Bauchi a karkashin bauchi state shari’ah Commission ta shirya yin muqabala da dr idris dutse tanshi kan wata kalma da ya fada akan manzon Allah.

An shirya yin muqabalar ne a 8 ga watan april amma daga baya sai gwamnatin ta sauke yin muqabalar bisa bukatar kungiyar izala da ta turowa chairman din Shari’ah kan ba lallai ne sai anyi wannan muqabalar ba.

Amma a bangaren dr idris akwai zargin yan dariqa su suka sa aka dakatar da wannan muqabalar hakan yasa a jiya asabar yan tijjaniya suka turowa chairman din Shari’ahr takarda kan cewa lallai a dawo da wannan muqabalar da aka shiryata a baya, ga abinda takardar ke kunshe a cikinta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!