SHARHI

Rahama Sadau – Ko mahaifiyarmu tasan nafi kowa fitina inji ta – abubuwa 10 da baka sani ba game da rahama Sadau

Abubuwa 10 Da Baka Sani Ba Game Da Fitacciyar Jaruma Rahama Sadau…Ko mahaifiyarmu tasan nafi kowa fitina inji ta! A yayinda tsohuwar korarriyar jarumar yar fim RAHAMA SADAU ke bikin murnar zagoyowar ranar haihuwarta a 7 ga watan Disamba 2016.

Rahama sadau
Rahama sadau

Abubuwa Goma da ya kamata ace duk wani masoyin jarumar ya sani game da ita.

1. Abu na farko shine ko kasan Rahama Sadau harkar kasuwanci ta karanta wato “Business Adminstration” a makarantar Kaduna Polytechnic?

2. Jarumar ta shiga harkar Fim ne a shekara ta 2013.

Rahama sadau
Rahama sadau

3. Fim din “Gani Ga Wane” ne farkon fim din da ya fara haska tauraruwar ta a duniya wanda tayi tare da fitaccen jarumi Ali Nuhu.

4. Kawo yanzu Jarumar ta samu lambobin yabo masu yawan gaske da suka hada da award din “Face of Kannywood a shekara ta 2016. “Best New Actress” a Landan a shekara ta 2015. “Best New Actress” a shekara ta 2014. “Best New Actress” a Bidbits Awards a shekara ta 2014. Sannan ta samu “Best New Actress” (Kannywood) a City People Awards shekara ta 2014.

5. Rahama Sadau ta kafa kungiyar taimakon marayu mai suna ”Ray of Hope”, wacce ta kaddamar a shekara ta 2016.

Rahama sadau
Rahama sadau

6. Rahama Sadau Produsa ce. Fim din kamfaninta na baya-bayan nan shine fim din “Rariya.”

7. A watan Octobar bana ne hukumar shirya fina-finai ta “Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria” ta sanar da korar jarumar daga Kannywood bayan da ta fito a wata wakar rungume ta wani mawaki dan Bauchi, ClassiQ “I love you” inda mawakin ya rika rungumar ta a cikin bidiyon wakar.

8. A watan Octoba ta tafi birnin Los Angeles na kasar Amurka domin amsa gayyatar da fitattun jarumai kuma mawakan Amurka, Akon da Jeta Amata sukayi mata domin ta kalli yadda suke daukar sabon fim dinsu mai suna “The American King.”

Rahama sadau
Rahama sadau

9. Hausa Times ta gano cewa Bayan zuwanta Amurka ta ziyarci wajajen shirya fina-finai da dama. Kuma ta yiwa Jarumi Akon rakiya zuwa taron karrama jaruman duniya na “Road to Redemption” wanda akayi ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba 2016, a Raleigh picture studios dake birnin Los Angeles.

10. Jaruma Rahama Sadau ta kware a yaren Turanci “ingilishi” da Hausa da kuma yaren idinyanci wato Hindi.

11. Hausa Times ta kuma gano Jarumar ta fito a fina-finan kudu na turanci wato Nollywood kamar fim din “Hakunde,” da

“Ajuwaya,” da kuma “Sons of the Caliphate.” A cikin wani hotonta da ta wallafa a shafinta

na Instagram da Facebook ta rubuta a jikin hoton cewa “Ko mahaifiyarmu tasan [ni Rahama Sadau] nafi kowa fitina” Yau ne jarumar ke bikin murnar zagayowar ranar haihuwarta!

Me zaku ce?

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!