KANNYWOOD

Duk Wanda Yace Yaushe Zangama Izzar So Baya Kishin Addinin Muslunci Cewar Lawal Ahamad

Duk Wanda Yace Yaushe Zangama Izzar So Baya Kishin Addinin Muslunci Cewar Lawal Ahamad

Shahararren jarumi nan mai farin jini lawal Ahmad wanda akafi sani da suna Umar Hashim acikin shirin Film ɗin Izzar So mai dogon zango ya bayyanawa duniya cewa, duk mutunenda yace yaushe zashi gama film ɗinshi mai dogon zango waton Izzar So, to yaƙalubalanceshi Akan cewa baya kishin addinin Muslunci.

Jarumin yafaɗi hakanne a wata takaitacciyar hira da shaharariyar Jaruma nan tayi dashi waton Hadiza Aliyu Gabon a zauren tattaunawa da fitattun jaruman Kannywood da take haskawa akowane sati.

Lawal Ahamad yabayar da hujja mai karfi dangane da wannan kalaman nashi, inda yake cewa. mutanenda suka musulunta ta dalilin Izzar So, basuda adadi duk dacewa basuda ɗinbi yawa amma yasan mutane huɗu da suka musulunta yanzu haka suna acikin garin Kano. Dan haka duk wanda keson agama Shirin film ɗin Izzar So to bashida kishin addini.

Bugu da ƙari jarumin ya sake bayyana cewa shirin Film ɗin Izzar So ɗinbin miliyoyin mutane ne kecin abinci a karkashin sa.

Film ɗin Izzar So Film ne mai dogon zango da ake haskawa a tashar ɗin bakori tv dake manhajar YouTube.

Umar Hashim ya amsa muhimman tambayoyi da Jarumar tayimasa. inda take tambayarsa cewa wanene ya maye gurbin daracta Nura Mustapha Waye. yace Aminu Al-Rahuz ne ya maye gurbinsa.

Acikin hira har ila yau jarumar tacigaba da tambayarsa cewa halin Umar Hashim nacikin Film da kuma halin lawal Ahamad duk ɗayane? inda jarumin ya bayyana cewa duk halayensane.

Jarumin yaƙara dacewa Shu’aibu Lawal Kwamarci da Abida Muhammad sune Jarumaina.

Dan asalin jahar Katsina ya bayyana cewa ɗaukada mutane keyiwa ƴan film amatsayin ƴan iska na ɗaya daga cikin abinda ke ɓata masa rayuwa.

Jarumin Yace Ali Nuhu da Hafiz Bello sune jarumai ko mutane da idan suka ce nadainayin abi ko nayi abi zanbi umurninsu. daga cikin biyun kuwa nafison Ali Nuhu.

Daga Karshe Jarumin ya bayyana halayen Ali Nuhu inda yake cewa Ali Nuhu yanada kirki, yanada fada da taimakon mutane.

Zumu cigaba da kawomuku wata sabuwar tattaunawa da sauran jaruman Kannywood kai tsaye acikin wannan shafin namu mai albarka.

Duk Wanda Yace Yaushe Zangama Izzar So Baya Kishin Addinin Muslunci Cewar Lawal Ahamad

Duk Wanda Yace Yaushe Zangama Izzar So Baya Kishin Addinin Muslunci Cewar Lawal Ahamad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!