LABARAI

Kwamandan Anti-thuggery Hon. Bello Bakyasuwa Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Kwamandan Anti-thuggery Hon. Bello Bakyasuwa Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Kwamandan hukumar yaƙi da ta’addanci ta jihar Zamfara, Hon. Bello Soja Bakyasuwa ya tsallake rijiya da baya daga hannun wasu ƴan bindiga da ake zargin anturosu ne domin su kashe shi, a hanyar sa ta zuwa Kaduna daga Gusau.

Manema labarai sun zanta da Hon. Bello Bakyasuwa inda ya ce, “Na tsira da rai, kwanaki huɗu da suka wuce a kan hanyata ta zuwa Kaduna ta hanyar Funtua-Zaria” wanda dama a kwanakin nan rayuwata na cikin haɗari, saboda hare – haren da nake fuskanta wanda ake zargin ƴan bindiga ne da wasu suka ɗauki nauyinsu.

A halin yanzu Bakyasuwa yana gadon asibiti yana jinya, rayuwarsa na cikin haɗari.

Bakyasuwa ya jaddada cewa lokacin da ya tashi daga Gusau zuwa Kaduna a cikin motarsa ​​ƙirar Hilux, ya lura cewa akwai motoci ƙirar Hilux guda biyu da motar BMW suna tahowa a bayansa.

Kwamandan Anti-thuggery Hon. Bello Bakyasuwa Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Kwamandan Anti-thuggery Hon. Bello Bakyasuwa Ya Tsallake Rijiya Da Baya

Ya ce, “Tunda naga yadda motocin da ke bayana suke bina jikina bai bani ba, don haka na tsaya a shingen bincike na Yankara, motocin suka wuce ni”.

“Na ci gaba da tafiyata, bayan na wuce garin Funtuwa da misalin karfe 8:30 na dare, sai na lura motocin Hilux da BMW ɗin sun dawo bina, daga bisani motar BMW ta bi ni sosai suka tare ni da ƙarfi a hanya”.

“Mutanen da ke cikin motocin ne kawai suka fara harbin motar da nake ciki kuma mun kwashe mintuna kaɗan muna musayar wuta da su.”

“Na yi tsalle na fita daga mota ta sakamakon raunin da na samu a ƙafata da kuma raunuka a fuskata”.

“Amma ƴan bindigar da nake zargin an ɗaukosu haya ne, sun ci gaba da harbe-harbe, nasamu nasarar tserewa na gudu na shiga daji da jini na fita daga jikina.

Hon. Bakyasuwa Ya ci gaba da cewa ya yi sa’ar ƴan sandan da suka isa wurin da jin ƙarar harbe-harbe suka cece shi.

Ya ce, “Lokacin da ƴan sandan suka isa wurin, sai suka yi gaggawar ceto ni, suka kai ni wata cibiyar kula da lafiya a matakin farko ta wani ƙauye da ke kusa.
Bayan na samu magani a asibitin na kwana a ƙauyen, sai da safe direbana da ya same ni a ƙauyen ya kai ni Kaduna don ci gaba da kula da ni”.

Bakyasuwa ya ce motarsa ​​ƙirar Hilux ta samu mummunar ɓarna sakamakon harbin bindiga da aka yi masa.
Ya kuma nuna ƙwarin guiwar cewa wasu ƴan siyasa ne suka ɗauki nauyin masu kai masa hari.
“A halin yanzu ina jinya a wani asibiti da ba a bayyana ba, kuma na yi imanin cewa ƴan siyasa ne ke ɗaukar nauyin maharan “.

Bakyasuwa ya koka da cewa, a watannin baya wasu ƴan bindiga sun kai wa direbansa hari a garin Gusau a kan hanyarsa ta daga Command Guest-Inn zuwa anguwar Gwaza inda suka ƙwace motarsa ​​ƙirar Hilux.
Ya kuma yi kira ga jami’an tsaro da su kawo masa ɗauki, ya ƙara da cewa rayuwarsa na cikin haɗari.

daga ƙarshe Hon. Bakyasuwa yace “Ina kira ga jami’an tsaro da su bincika su kama waɗan da suka kai harin”.

Allah yatsare gaba, ya bashi lafiya, Allah yaba jaharmu ta Zamfara zaman lafiya mai ɗorewa, Amin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!