TATTAUNAWA

Tattaunawa da shamsu Dan lya da dalilin da yasa yake yawan kuka da zai matukar baku mamaki

Kana tunawa da wani abune idan kana kuka ?


Eeh to ! Il owanne jarumi yana da salon kukan sa, kamar ni gaskiya ba komai nake tunawa ba, kawai kirkirowa nake. Wani. Lokacin kuma idan aka bani dialogue din na tausayine, to alokacin ma da nake fadan shi, alokacin ma danake fadanshi nake kuka ba sai anjira na kirkiro ba. Wasu hamma sukeyi, yanzu kaga kamar Ahmad Ali Nuhu, idan zaiyi kuka a fim, ruwa kawai yake cewa a bashi, da zarar ya sha, sai fara kukan. Ko waye da salon sa.

Meyasa kake yawan kuka a fim din soyayya ?
Anzo gurin. Ana yawan yimini wanan tambayar, wasuma da zarar sun ganni sai kaji suna cewa “ga me yawan kukan nan”. Wato abin da yake faruwa shine, kasan duk abin da akace soyayya, akasari zaka ga ina fitowa ne a rol din soyayya kuma shi soyayya abu ne wanda yake da ciwo. Akwai lokaci Ahmad S. Bono muke magana da shi, yake cewa “abin da yasa idan kana fim, kana tabawa mutane zuciya shine, kana da sifar maza, ma’ana kamalar ka gaba daya ta maza ne. Mutane suna ganin cewa duk abin da zai sa namiji kuka, to lallai wannan abun abune mai matukar ciwo. Ya kai ya sa shi kuka. Saboda yanzu idan ina acting fim d’un soyayya, yawancin “coleague” dina wanda suke bayan kamara, idan ina kuka, su ma kuka sukeyi, saboda yanda nake “sharing feelings” dina, ya na matukar tabasu.

Wane abu ne yafi baka farin ciki ?
Abin da yake matukar sani farin ciki shine duk lokacin danake “location” tare da “coleague” dina, ina matukar samun farin ciki saboda yadda muke zolayar juna, da wasa da dariya. Wannan shine lokacin da nafi samun farin ciki.

Me yasa ake ce maka Dan lya ?

Sunana Shamsu Dan lya, an haifeni a garin Kaduna, nayi karatuna na matsayin digiri a Maryam Abaca University(MAU), na karanta Maths/Communication. Abin dayasa ake kirana Dan lya sunan sarautar Kaka nane, shikuma kakana shike ce min Dan lya, shikuma kakana shi din Iyan kyale ne. Shiyasa ake cemin Dan lya.

Wace kyauta aka taba yimaka da baza ka manta da itaba ?

Gaskiya ! Lokacin da sarki ya bani kyautar mota. Wannan itace kyautar da bazan taba mantawa da itaba.

Wane ne Sarki ?

Hahaha ! King of Kannywood mana. Saraki. Kasan shi sunayensa sunfi dari, Nazifi Asnanic yana kiransa kajangu, wasu suce yallabay wasu suce Sarki…

Wane abun bakin ckine da baza ka manta da shi ba ?
Abun bakin cikin da bazan manta da shi ba, wani abu ne da baza kaso kafito ka gayawa al’umma ba. Wanan shine.

Wace ce budurwarka ta farko ?

(Waka)” randa na fara ganinki Fatima, ran asabarne kin ci kwalliya”. Idan ka rike wanan wakar, inaga itace budurwarta ta farko. Kamar yadda mutane suka sani, wannan shine.

Shekarar ka nawa ?

Shekaruna yanzu 31 .

Ya batun aure ?

Me niya ne dai, ina da niya amma ba ni cewa gashi.

Mata nawa kake da niyyar aura ?

Ni mutumne wanda ke da niyyar aurar mace daya. Mace daya nake so na aura gaskiya.

Mece ce wahalar aikin sauti ?

Wato lokacin da nayi aikin sauti, gaskiya aikin ya fi waha saboda a wannan lokacin babu irin wireless da muke aiki dashi.

Bayan aikin sauti kana da wata boyyayyar baiwa ?

Eh bayan aikin sauti ina wasan kwalo sannan na iya iyo(swemming).

Wacce kungiyar kwalo kafa kake goyon baya ?

Ina goyan bayan Manchester United wato the red devils

Wane tambayaba masoyanka suke yawan yimaka

Tambayar da muta ne suke yawan yimini itace, “yaushe zakayi aurae?*

To yaushe zakayi auren ?
Gaskiya bazan iya cewa ga lokaci ba sai dai idan lokacin yayi kawai a gani, watikila ma sai nayi a sirrance sai dai kawai aji ni da matata a wata kasar.

Thanks for your kind attention !!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!