KANNYWOOD

Tattaunawa Da Baba Ɗan Audu Akan Magana Aurensa Da Jaruma Hadiza Shema

Tattaunawa Da Baba Ɗan Audu Akan Magana Aurensa Da Jaruma Hadiza Shema

Acikin shirin namu nayau zakuji cewa shahararen jarumin nan na masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood Rabi’u Rikadawa wanda kunkafi sani da suna Baba Ɗan Audu Acikin shirin Labarina ya bayyana cewa yanason hadiza Shema.

Jarumin yafaɗi Hakanne awata hira da jaruma Hadiza Aliyu Gabon tayi dashi akan abinda yashafi rayuwarsa.

Inda Jaruma Hadiza Aliyu Gabon take tambayarsa da cewa ya soyayyashi da Jaruma Hadiza Shema ta kasance ?

Jarumin ya amsa tambayarta inda yake cewa soyayya su tananan kuma idan lokacin aure yayi atsakaninsu za’ayi.

Jarumin tacigaba da cewa idan kuma akakai wani lokaci da tayi masa tsufa to zaya canza wata.

Rabi’u Rikadawa yakasance shahararen jarumin a masana’antar Kannywood inda yafi kwarewa awajen fitowa talaka mai son kuɗi Musamman acikin shirin Film ɗin Labarina da ake haskawa a tashar Saira Movie dake manhajar YouTube.

Acikin tattaunawa da Jarumin dai Jaruma Hadiza Aliyu Gabon tacigaba tambayarsa, inda take cewa miyasa basa saka ƴaƴansu acikin shirin film ?.

Rikadawa ya amsa dacewa, ai yanzu haka ɗiyarsa tana cikin wani film da ake haskawa ahalin yanzu. hasalima mijin ɗiyarsa ɗan film ne, dan haka duk wanda yace bamuba ƴan film ɗiyanmu to ƙasar yakeyi.

Daga karshe Jarumin Rabi’u Rikadawa ya fitarda sanarwa akan cewa kwanana zai fito da wani sabon Film ɗin sa wanda zai rinƙa haskawa a tashar sa dake manhajar YouTube.

Baba Ɗan Audu yayi kira da mutane wayanda basa fahimta yanda zasu banbance harka film dakuma harka rayuwa bayan film akan sirinka yimusu uzuri akan yanayin aikinsu.

Daga karshe dai Rabi’u Rikadawa yabayana cewa Falalu A Ɗorayi shine gwaninsa a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood baki ɗaya.

Domin kallon cikakkiyar hira da jarumin ta hanyar bidiyo, zaku iya ziyarta tashar Hadiza Aliyu Gabon dake manhajar YouTube kai tsaye.

Tattaunawa Da Baba Ɗan Audu Akan Magana Aurensa Da Jaruma Hadiza Shema

Tattaunawa Da Baba Ɗan Audu Akan Magana Aurensa Da Jaruma Hadiza Shema

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!