KANNYWOOD

Hira da Ali Nuhu Ya Bayyana Abinda Ƴaƴansa Sunkafi So

Hira da Ali Nuhu Ya Bayyana Abinda Ƴaƴansa Sunkafi So

Abin da ya sa nake bin ra’ayi ƴaƴana game da rayuwarsu

Acikin Shirinmu nayau zakuji cewa Fitaccen tauraron fina-finan Hausa na Kannywood Ali Nuhu ya ce inda don ta shi ne ya fi so ɗansa ya gaje shi a harkar fim.

To amma kuma a cewarsa ɗan nasa ya fi sha’awar harkar ƙwallon ƙafa, dalilin da ya sa kenan ya mara masa baya, domin ya cimma burinsa da yakeso cimawa arayuwar duniya.

Ali Nuhu ya ce ”abin da zamani ya zo da shi yanzu shi ne, idan ka ga ɗanka ko ‘yarka na son wani abu, matuƙar bai saɓa wa addini ba to ka goyi bayansa, ka ba shi ƙwarin gwiwa wajen cimma burinsa.”

Ya ƙara da cewa kar ka tilasta wa yaro kan dole cewa sai ya yi wani abu.

Jarumin ya bayyana cewa itakuwa ƴar sa Fatima Ali Nuhu Tafison harka Social Relationship. hakan yasa tafi zakewa wajen yin karatu a jami’a. kuma yanzu haka tafi samun maki mai ɗinbin yawa acikin abukanin karatunta.

Hira da Ali Nuhu Ya Bayyana Abinda Ƴaƴansa Sunkafi So

Photo:Hira da Ali Nuhu Ya Bayyana Abinda Ƴaƴansa Sunkafi So

Zamu kawomuku hira da mukayi dashi acikin bidiyo kai tsaye domin ganin yanda takaya da fitacen jarumin.

Kucigaba da bibiyar wannan shafin namu mai albarka domin samun sababbin shirye-shirye mu akan lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!