SHARHI

Jerin jaruman kannywood da mummunar jarrabawa ya same su a rayuwa da ba’a fatan wani ya same shi.

Jerin jaruman kannywood da mummunar jarrabawa ya same su a rayuwa da ba’a fatan wani ya same shi.

1- SANI IDRIS MOƊA

Jarumi, Sani Idris, da aka fi sani da ‘Moda’ ya dade ya na kwance a asibiti, karkashin kulawar likitoci, bayan ciwon da ke damunsa ya yi tsanani. Moda na fama da matsanancin ciwon sukari (Diabetes), kuma an kwantar da shi a asibiti tun cikin shekarar da ta gabata. Halin da jarumin ke ciki ne suka jawo wasu kafafen yada labarai da ma’abota rubutu a dandalin sada zumunta suka fara jita-jitar cewa Moda ya mutu a cikin watan Mayu na shekarar 2018, kafin daga bisani ya fito ya bayya cewa yana nan da ransa.


Daga karshe dai an yanke wa fitaccen jarumin fina-finan Hausa, Sani Idris, daya daga cikin kafafunsa sakamakon rashin lafiyar da ke damunsa.

Tun bayan kwantar da Moda, manyan jaruman fina-finan Hausa da suka hada da Ali Nuhu da manyan darektoci irinsu Falalu Dorayi ke zarya zuwa asibitin da aka kwantar da shi domin duba lafiyarsa.

Moda na daga cikin jaruman fina-finan Hausa da suka dade an dama wa da su a masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood). Jarumin ya samo sunan ‘Moda’ ne sakamakon rawar da ya taka a wani tsohon shirin wasan Hausa mai suna ‘Wasila.

 

2- HAMZA YAHAYA

Hamza Yahaya dai ya hadu da ibtila’a ne na yan bindiga shi da abokinsa mai suna Ataka, inda yan bindigar suka bude musu wuta, lamarin da yasa harsashi ya wuce ta gefen hancin Hamza wanda ya haddasa mai mummunan rauni akan hancin.

Bayan an masa aiki ne sai yanzu kuma baya iya numfashi yadda ya kamata, Hakan yasa baya iya bacci ko kadan. Wasu daga cikin jaruman Kannywood sun nemi gwamnati ta temakawa Hamza domin ai masa aiki.

Sai Sanata Barau I Jibril Maliya ya dauki nauyin kai jarumin kannywood hamza kasar waje domin ai masa aiki a hancin nasa.

wannan abu ba karamin dadi yayi jaruman Kannywood ba kasancewar sanata ya nuna suna da muhimmanci a garesu.

 

3- TIJJANI ASASE

Tijjani asase dai yana daga cikin jaruman kannywood da suka goya kannywood a baya har ta kai wannan matsayin da take kai a yanzu, ya saba fitowa a dan daba a finafinai.

A shekarar 2018 gobara ta tashi a gidan tauraron fina-finan Hausa, tijjani Asase, ta kone komai kurmus, ba’a fidda komai ba, amma shi da iyalanshi sun fita lafiya kamar yanda ya sanar.

Washi garin ranar da abi ya faru, Jarumin shi ya sanar da faruwar al’arin ta inda ya daura hotunan gidan nasa bayan ta kone a dandalin sada zumunta yayi rubutu kamar haka akai ”Ina lullahi wainna ilayhirraji’un Adaran jiya musalin karfe dayan dare gidana yakone babu abida ya fita sai iyalina Allah yamayarmin da Abinda akai asara Amin”

 

4- ASHIRU NAGOMA

Ya kasance babban darakta ne a kannywood da a baya yayi tashe sosai, amma daga baya sai Allah ya jarabbace shi da ciwon hauka.

A wata hira da marubuciya mai suna Fauziyya D Sulaiman da tayi da bbc hausa tace ƴan uwan Nagoma sun ce mata abin ya samo asali ne tun shekarar 2007 lokacin da bidiyon Maryam Hiyana ya yaɗu.

“To a cewarsu a lokacin ya saka kuɗaɗensa ya yi fina-finai wajen bakwai, sai lamarin ya faru inda hukumar tace fina-finai ta ce kar a sake sakin fim ɗin da Maryam Hiyana ta fito a ciki.

“A lokacin ne fa ya shiga ruɗani don rashin madafa ganin cewa ya narka kuɗi ya yi fina-finai da ita, amma dole zai yi asararsu tun ba su fita kasuwa ya mayar da kuɗi ba balle cin riba.

“Lamarin dai ya dagule masa ga asara da ya tafka wacce dole ta sa ya janye daga masana’antar, a hankali damuwar ta dinga tsananta har ta taɓa masa lafiyar ƙwaƙwalwarsa,” in ji Fauziyya.

Ashiru Nagoma dai ɗan asalin jihar Kano ne kuma bai taɓa aure ba,

An samu damar kai Ashiru asibiti ne bayan rasuwar mahaifiyar sa da a baya taki a kaishi asibitin, kuma bisa ikon Allah sai ya samu sauki.

 

5- AMINU ILU DAN BAZAU 

 

wanda akafi sani da Aminu acid tsohon jarumi ne wanda shima ya jima acikin Masana’antar, yayi fice matuka sannan tauraronsa ya haska ne acikin film din Al’ajabi wanda Suka fito tare da Fati Muhammad.

Sai dai jarumin ya kwashe wasu shekaru rabon da aga fuskar sa acikin finafinai, amma daga baya yaci gaba da harkar inda yana daya daga cikin jaruman shiri me dogon zango na Labarina wanda malam aminu saira yake gabatarwa

Amma bayan dawowarsa cikin Masana’antar yawancin finafinan sa yana fitowa ne a matsayin likitan lafiya. A shakara ta 2020 jarumin shima Allah ya jarabceshi da gobara a gidan sa wanda tayi Sanadiyyar kone komai da aka mallaka a gidan, sai dai shima Allah ya kubutar da iyalansa.

 

6- SAFIYA YUSUF SAFARA’U

A shekarun baya ne wani bidiyon tsiraicin jarumar kannywood mai suna safeeyah yusuf wacce aka fi sani da Safara’u ya yadu a duniya

Bayan faruwar al’amarin Safara’u

ta ce ta shiga mawuyacin hali bayan faruwar lamarin inda ta kai har wata uku ba ta fita ko waje ba, har ma ta kai ana jifan ta da duwatsu idan ta zo wucewa ta wani wuri.

Ta bayyana cewa mutane da yawa sun ce tayi abin ne domin tura wa wata kawarta da suke madigo tare inda wasu kuma ke cewa ta aika wa saurayinta bidiyon ne.

Ta ce dukkan ‘yan uwanta sun ce mata wannan kaddara ne na rayuwa kuma ta dau dangana, amma mutanen gari ke tsinuwa suka yi ta mata da kuma kiranta da sunan karuwa wanda har ta kai ga ta kusan toshe dukkan shafukanta na sada zumunta.

 

7- AMINU AHLAN

Wasu matasa da ake kyautata zaton ‘yan daba ne, sun Sassari fitaccen dan was Ahlan da adda a gefen goshin sa, da gadon bayan sa. Sanadiyya wannan sara da aka yi masa, Ahlan ya samu mummunan rauni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Content is protected !!